A GANINA:
daga John E. Philips, Yabase, Akita, Jafan
Da Muhammadu Bello d'an Usuman d'an Fodiyo ya zama Sarkin Musulmi sa'adda Mahaifinsa Shehu Usuman d'an Fodiyo ya rasu, sai fitina da tawaye suka tashi. A Kano D'an Tunku, Sarkin D'ambatta ya yi tawaye har an ba shi sarautar Kazaure. A Katsina akwai tawayen Marad'i wanda ya dad'e har zuwan Turawa. Ko a Sakkwato da kanta akwai tawayen Abdussalami daga garin Kware.
Maganin wad'annan tawayu shi ne zaman ribad'i. Da ilminsa na tarihi,
da na zaman jama'a a Musulunci, sai Bello ya kafa ribad'i a ko'ina.
Ya yi zaman ribad'i daga lokacin da ya zama Sarkin Musulmi har ya rasu.
Da Shehu Usuman ya rasu nan da nan Bello ya sake gida zuwa Karandai.
Daga Karandai ya sake gida zuwa Magarya. Daga Magarya ya sake gida
zuwa Wurno. Ya zauna Wurno har an ba shi lak'abi "Mai Wurno" kuma
an yi masa kabarinsa a Wurno inda ya rasu. Wazirin Sakkwato Alhaji
Junaidu ya fassara abin da Bello ya gaya mana da ya ce "Hak'ik'a mazaunin
ribad'i inda ya rasu, nan ake binne she cikinsa, ba a nad'a takardarsa.
Ana rubuta masa lada kullum kwatankwacin kamar abin da ake rubuta masa
yana rayayye har ranar tashin alk'iyama."
Menene zaman nan na ribad'i, wanda Bello ya yaba haka? Gaskiya,
asalin kalmar daga Alk'urani ne. A cikin Surat Al-anfal (8:60) an ce "Wa
`aciduu lahum maa istatctum min qawah wa min ribaat al-khayl." Wannan
aya ta gaya wa Musulmi su yhi d'amarar yak'i, su sami dawakin yak'i.
Daga baya, da Larabawa suka ci k'asashen gabas ta tsakiya da kuma Afirka ta arewa, sai suka koyi yadda su Rumawa suke ginin gidajen tsaren iyakar k'asashensu. A Larabci an ba irin wannan ginin nan da sunan "ribaat". Akwai masallaci da kuma d'akuna don zama da kuma don tanadin makamai.
Da Turawa suka fara korar Larabawa daga Alandalus (Hispaniya) sai Larabawa suka shiga zaman ribad'i don su hana korar. Da suka taru a Afirka ta arewa, sai suka ci gaba da ginin ribad'i har aka kafa daular da Turawa suka ba su sunan "Almoravid." Da Larabci ana ce mata "al-muraabit" watau "mazaunin ribad'i". Wannan daula ta bangaje Turawa har ta yi sarautar Hispaniya a k'arni na 11 da 12.
Da Larabawa suka zauna a Afirka ta Arewa, sai zaman ribad'i ya zama zaman sufantaka. 'Yan d'arik'a sun zauna ribad'i don su yi addu'a. Har yanzu a Larabcin Afirka ta arewa, ma'anar "ribad'" da ma'anar "zawiya" duk d'aya ne.
Muhammad Bello ya fi sanin tarihin Musulunci ya karanta littattaffai da yawa har ya fahimci irin ribad'in gargajiya a k'asashen Larabawa. Littafin da ya fi so a kan batun ribad'i, shi ne Masharic al-Ashwaq na Ibrahim al-Dimashqi. Bello ya tsakuro littafin a littafinsa mai suna "Al-Ribat wa'l-Hirasa". Za a ga littafin Bello a Jami'ar Ibadan da Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya inda aka ajiye littattafan tarihi.
Bayan littafin ya rubuta wasik'u zuwa mutanen da ya nad'a sarakunan ribad'i. D'aya daga cikinsu muhimmai shi ne k'anensa kuna magajinsa Abubakar Atik'u. Bello ya akia masa da wasik'a sa'annan ya sa shi mayar da garin Bakura ribad'i a shekarar 1836 kusa da k'arshen mulkin Bello. Bakura ta goyi gayan tawayen Abdussalami, shi ya sa Sarkin Musulmi Bello ya yi kaffa kaffa da ita.
A farkon wasik'ar Bello ya tuna wa Abubakar cewa ya yi koyi da wata d'abi'a muhimmiya daga Musulunci. Ya ce su yi iyakar k'ok'ari su shirya, su ja d'amarar yak'i su had'a masu dadi da 'yan lek'en asiri da jarumai da kuma dawaki da ruk'uma. Ya ce dole su shirya yin kamun ganima da makamai a ko da yaushe.
Shawarar Bello ta biyu, ta tuna wa Abubakar da cewa, ya mayar da himmja ya yi godiya ga Allah saboda Allah ya ba shi sarautar ribad'in nan. Ya ce Allah ya umarci masu mulkin duniya su yi sallah, kuma su ba da zakka su umarci a yi aikin alheri kuma su haramta mummunan aiki. Ya ce Abubakar ya yi hankali da kafirci kada Allah ya k'wace sarautarsa har ya bari a washe garin.
Shawara ta uku, Bello ya ce ya k'arfafa amana da ahalil kitabi. Ketawar amana da ahalil kitabi ita ce d'aya daga cikin manyan k'azamin miyagun laifuffuka. Mai yin ta zai had'u da tsananin hukuncin duniya da na lahira. Ya ce kada a d'auki komai daga ahalil kitabi ban da jizya, ko da kaza guda d'aya ce.
Ta hud'u, Bello ya ja kunnen Abubakar saboda jarrabar gari. Bello ya damu kada karuwai su cika garin. Ya ba da shawarar a daina jin dad'in k'wara k'warai, a maimakon haka sai a yi rawar daji.
A k'arshe Bello ya gargad'i Abubakar da mabiyansa da su yi k'ok'ari su sake ginin garin kuma su sake shuka. Raba mutum da gonar da ya mallaka ba muhimmi abu ba ne. Abu ma fi muhimmanci she ne ni'ima. Idan wani ya zo yana neman wurin gayauna sai a ba shi har garin ya yi albarka. Da wannan albarka ta samu, sai mai gona ya mallaki abinsa, amma kafin gari ya cika kada a raba k'asa.
Shari'a ita ce hanyar zaman lafiya da samun alheri a duniya. Wad'annan su ne manufar shari'a.
Bello ya rubuta wa d'ansa Fodio wasik'a sannan ya ajiye shi a ribad'in Lajinge a iyaka da Gobir. Ya ja kunnensa ya kulle iyakar, kuma ya tsare hanyoyi. Tilas ya tura a kai hari kuma ya kai 'yan leken asiri. Bello ya gargad'i d'ansa ya tabbatar da shari'a kuma ya tabbatar da adalci. Kada ya zagi wani, kada ya d'aure wani kada ya kashe wani mutum, ban da tsananin zartar da shari'a.
A ra'ayin Bello shari'a ita ce hanyar zaman lafiya a duniya. Bello ya ba Fodiyo umurni, cewa kada ya ci hanci ko ya ci haraji ko ya yi gadara. Sai dai ya gayar da malamai kuma ya saurari nasiharsu. Ya kamata ya taimaki matafiya (musamman zuwa Hajji) kuma ya taimaki matalauta. In Fodio bai bi umurni ba, ko mutanensa ba su bi shi ba, za a tub'e shi. Gaskiya fa, a k'arshe an tub'e Fodio saboda mugun mulkinsa.
Mulkin Bello ba mulki ne na dangi ba. Ya aika wa Yak'ubu Sarkin Bauci da wasik'a. Ya bayyana masa yadda zai ci gaba da mulkin Musulunci. Ya gaya masa sai a sa Fulani a ribad'i ko su bar shanu da dausayi. A ra'ayin Bello ak'idar Musulunci ta fi k'abilanci klo dangantaka.
Wannan manufar ribad'i ta Bello tana da dalilai dabam-daban. Bello na son a tare birane da hanyoyi. Kuma ya tsara a saki jami'a. Ya sa Fulani a garuruwa a k'arkashin malamai. Ya had'e Fulani da Hausawa da bayi. Dukkansu sun koyi harshen Hausa, har ya zama harshen k'asar da sabuwar jama'arta. Bello ya cika k'asa da sababbin garuruwa masu nisa da tsofaffin garuruwa. Ya k'arfafa Musulunci da ilminsa. Ya k'arfafa shari'ar Musulunci don a daidaita adalci kuma a hana k'abilanci.
Bello ya zauna ribad'in Wurno, kuma ya sa shi ya zama cibiya don ya
nuna wa sarakunan da ke k'arkashinsa yadda za a kafa ribad'i da kuma yadda
za a kafa ribad'i da kuma yadda za a gudanar da ayyukansa. Daga wannan
bayani mun ji labarin ribad'in Bello a Wurno.