GASKIYA TA FI KWABO   (Kaduna, Nigeria) 24 ga Maris, 1994  shafi na shida

A GANINA:
 

Da Wannan Abu ya Samu, da K'ila Yanzu Birnin Kano na Takai' --In Ji Alhaji Abubakar Dokaji (Kano ta Dabo Cigari)

daga John E. Philips, Yabase, Akita, Jafan



 
    Mene ne abini nan wanda ya kusa sanarwa har watak'ila garin Takai ya kusa ya zama Birnin Kano?  Wannan abu kuwa shi ne niyyar Sarkin Kano Babba Zaki (1768-1776) da ya yi na ya sake gida zuwa Takai.  Shi ne dai ya gina gidan Sarkin Kano a can garin.  Ya ko yi niyyar tarewa can, har garin ya zama babban birnin Kano, amma mutanen fadarsa suka k'i.

    Duk da haka yawan manyan sarakunan Kano sun zauna a gidan sarkin Kano a garin, misali, Sarkin Kano Alwali (1781-1807), da Sarkin Kano Abdullahi "Sarkin Yanka", da d'ansa Yusufu.  Da Yusufu ya yi k'ok'ari ya  zama Sarki a zamanin yak'in Basasar Kano sai ya sa cibiyarsa a Takai.  Lallai akwai tarihi sosai tattare da garin.

    Sarkin Kano Muhammadu Sharif (1703-31) ya kafa ribad'i a Takai.  Ribad'i fa, irin birnin nan ne mai ganuwa ne.  Kalmar daga Alk'urani aka same ta.  Ma'anarta a harshen Hausa, ita ce gari don tsaron iyakar k'asa ko tsaron hanya.  Akwai sifar murabbi'i na kallon alk'ibila ga ribad'i.  Ana cika garin da jarumawa a Tsakuwa, da Gano, da Dawaki da sauran garuruwa na k'asar Kano ta Kudu maso Gabas.  Takai ta fi nisa daga Birnin Kano, daga duk cikin garuruwan.

    Sarkin Kano Babba Zaki wanda ya kafa gidan sarki a Takai, shi ne babban jarumi.  Yayin yak'i a ko'ina a koyaushe.  An yi yak'i sosai a garin Takai a lokacin.  Watakila wannan shi ne dalilin da ya sa Babba Zaki ya so ya mayar da gidansa zuwa Takai.  Daga zamaninsa sarakunan Kano sun je Takai don su bar 'Dawainiyar fadarsu, su yi hutu.  A cikin wani lokaci ne daigarin ya cika da gidajen bayin sarki.

    Banda bayin sarki garin Takai ya cika da malamai.  "Husaini na Takai" shi ne d'aya daga manyan malaman Sarkin Kano Babba Zaki.  Malamin da ya fi kowa a cikin malaman Takai mashahuranci, kuwa shi ne Malam Manciyau.  Malam Manciyau ya koyar da karatu a masallacin Juma'a.  "Bawan Allah" ne har Allah ya sa ya fahimci maganar babbobi ya zama alk'alinsu.  Da ya rasu an rufe shi a masallacin Juma'a.  An gina sabuwar masallaci.  Tsohuwar masallacin ya rushe ya zama hubbarensa.  Albarka daga hubbaren ta dad'e a k'asar har yanzu.  In ba a yi ruwa a garuruwan da ke kusa da Takai ba, to, mutane za su taru a hubbaren Malam Manciyau su yi addu'a.

    Akwai malamai da yawa daga Takai, misalin shi ne Malam Alhaji, da Malam Kacalmu, da Malam Sirri da Malam Salihu, da Malam Zanema da kuna Malam Shekarau wanda ya warkar da hannun Alwali da ya yi musabaha da shi don gaisuwarsa.  Babu dama a gaya maku duk labarunsu yanzu.  Amma in za a je Takai za a ji labarun, ko za a ga d'akin Alk'uranin Malam Zanema.  In an sab'a laya da Alk'uranin nan akan k'arya, to za a mutu.

    Labarin Malaman Takai wanda ya fi shahara, shi ne labarin ziyarar da Usuman 'Dan Fodiyo ya yi zuwa Takai a zamanin Sarkin Kano Alwali.  Shehu ya tambayi malamin ko zai koyar masa da ilmin hisabi.  Malamin ya ba shi amsa cewa ilmin hisabi mai tsada ke nan, amma shi Shehu ya yi shigar talakawa ne.  Shehu ya ba da amsa cewa zai ba da sauran darasi a kan hisabi.  Ya tambaye shi ya rintse idonsa.  Da ya bud'e idon sai ya ga sun tashi zama.  Ya sake rintse, wa ya bud'e, sai ga shi sun komo k'asa.  Nan da nan ya gargad'i Sarkin Kano Alwali cewa akwai karama wadda ta iya bamb'are mulkin daularsa.  Sai dai babu wata shaida mai gamsarwa cewa Shehu Usman 'Dan Fodiyoya tab'a zuwa Kano, balle Takai.  Duk da haka labarin shi ne shaida cewa Takai garin ne muhimmi kuma mashuhari ko kafin zamanin jihadin Shehu Usman 'Dan Fodiyo.

    An tabbata cewa Sarkin Kano Alwali yana gidansa a garin Takai  sa'ad da Jihadi ya b'arke kusa da Bebeji.  Mai Garin Bebeji ya aika masa da wasik'a, cewa Sufawa masu talauci wad'anda suke koyon ilmi a k'ark'ashin manyan malaman birni., sun had'u sun tashi har sun watsa mutanen gari sun washe dukiyarsu.  Da jin labarin sai 'yan 'uwansa suka tashi suka gama kansu a Takai.  Ba su komo Birnin Kano ba har aka ci su a farkon yak'i.

     Malam Bakatsine, Sarkin Job'awa, shi ne shugaban masu jihadi a Kano ta Kudu maso Gabas.  Shi da mutanensa sun ci Gogelo da kuma Gaya da sauran garuruwan da ke kusa.  Sa'ad da ya ci Takai har mutanen garin suka watse.

    Daga zamanin hadi zuwa zamanin tawayen Ningi, ba a ji labarin Takai ba har yanzu.  Da Malam Hamza ya fara tawayen Ningi sai Sarkin Kano Abdullahi ya sake gina gidan Sarkin Kano a Takai.  Ya aika d'ansa Galadima Yusuf da sauran manyan jarumawa su je Takai ko sun k'i ko sun so.

    'Daya daga cikin wad'annan jarumawa shi ne Maisaje.  Shi Galadiman Makaman Kano ne.  Yana so ya gaji saraurtar Makama.  Da ya ji labarin za a kai shi Takai sai zuciyarsa ta b'aci.  Duka da haka ya je, ya yi yak'i sosai amma ba a cinye Ningi duka ba.

    A ranar 7 ga watan Yuli na shekarar Masihiyya 1862, Dakta W. B. Baikie ya ziyarci Takai.  Ya ce garin yana da ganuwa da gwalalo.  Akwai mutane kamar 1,500 a ciki, garin dai bai kai girman Dutse ko Gaya ba, amma garin Takai shi ne d'aya daga manyan garuruwan sashen.

    Da aka nad'a Sarkin Kano Muhammadu Bello, a kowance shekara sai ya tura d'ansa Muhammadu Tukur zuwa Sakkwato don yin jihadi a lokacin rani.  Da Tukur ya kai hari Kila da Gurum, Sarkin Musulmi Abdurrahman ya yi murna.  Saboda yak'ikn da Tukur ya yi a yak'in Argungu, Abdurrhaman ya gaya masa "Goronka Kano da ta fad'i."  Wannan magana ita ce tushen yak'in Basasar Kano.

    Da Sarkin Kano Bello ya rasu sai Abdurrahman ya ba da umarni a nad'a Tukur.  Yusufu d'an Sarkin Kano Abdullahi ya yi fushi saboda yana so a nad'a shi Sarkin Kano.  Shi da d'anuwansa da mabiyansu sun tashi sun had'u sun nufi Takai.  Da suka isa [ . . . ] yi shawarar cewa, Sarkin Takai Umaru d'an Maisaje ya gaida Yusufu, amma Limamin gari ya k'i.  Limamin da mabiyansa sun tashi sun bar gari.

    Yusufu da mabiyansa a Takai sun aika wa garuruwa da wasik'u.  Sun tambaye su su goyi bayan maganar Yusufu, wanda bai yarda ba, aka ci su da yak'i.  Daga Takai mabiyan Yusuf sun ci Da'u, da Gamsa, da Katanga da Birnin Kudu da Katanga Gabari da Katanga Kazuba da dai sauransu.

    Tukur bai fito fadarsa a birni ba.  Sai ya tura wakilansa su shirya tsaron garuruwa.  Ya fi yin kyauta ga malamai amma ba yi yak'i ba.

    Bayan haka Yusufu da mabiyansa sun ci Gaya.  Wannan Gaya dai babban gari ne a gabashin kano ne.  Daga nan garuruwan da dama sun bar goyon bayan Tukur, sun shiga goyon bayan Yusufu.

    Sarkin Takai Umaru muhimmi na a yak'in Gaya.  Saboda haka Yusufu ya ce masa, "Wannan ya wuce dagaci, a yi masa hakimi."  Ya nad'a Umaru Sarkin Gaya.

    Bayan haka Yusufu ya kama ciwo.  Ya nufi Takai amma ya rasu a Garko.  A Takai an nad'a k'aninsa Aliyu ya zama sarki.  Aliyu ne ya k'are yak'in basasa.

    Da Aliyu da mabiyansa sun shiga birnin Kaon sai Sarkin Kano Gaya Umaru d'an Sarkin Takai Maisaje ya kai wa Gidan Rumfa farmaki.  Don goyan bayansa a kan maganar Yusufawa Sarkin Kano Aliyu ya nad'a Umaru d'an Maisaje sarautar Makaman Kano.  Wannan babbar sarautar Job'awa ce wadda mahaifinsa ke so.  Gidan Umaru a Birnin Kano ya zama gidan kayan tarihi a birnin Kano, kuma mashahuri mai suna "Gidan Makama."

    Da Aliyu ya zama Sarkin Kano, ya dinga ginin ribad'i da kuma k'arfafa su.  Ya kai wa Ningi hare hare da dama.  C. H. Robinson, wanda ya ziyarci birnin Kano a zamanin Aliyu ya tabbatar da yawan bayin da Aliyu ya kawo daga Ningi, ya ce sun fi dubu.  Lallai akwai fiye da haka a rinjin Sarki!

    Mutanen Takai su ma suna yak'i da na Ningi a zamanin.  A yak'in Rumo, a daf da Sumaila, mutanen Takai sun yi wa sansanin jarumawan Ningi kwanton-b'auna.  An kama mutanen Ningi da yawa an kai su Takai sun zama fursunonin yak'i sun kuma zama bayi.

    A waniyak'i da Ningi a zamanin Sarkin Takai Umaru, da jarumawansa suka dank'e tambarin Ningi.  Sun kai tambarin gidan Sarkin Takai.  Suna nan har yanzu.  Duk wanda ya ziyarci garin a ranar Sallah, zai ji tambarin Ningi.  Takai ba babban birni ba ne, amma gari ne mai tarihi sosai, yana da girmansa, yana da martaba, yana da tambari kamar yadda ya kamata duk gari mai gidan sarki ya yi.
 
 



 
back to essays
 
back to homepage